Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da ‘kiran Imam Sayyid Aliyul ga Iraniyawa da su fito kwansu da kwarkwatansu a ranar 11 ga watan Fabrainu, fiye da ko wani lokaci don nuna goyon baya da kuma karfin jmi a dai dai lokacinda yake cika shekaru 47 da samun nasara. Wanda ni tahir amin zana karanta .
///..madallah, A ranar litinin ce Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminaei ya fito a kafafen yada labarai a nan Iran, yana kira ga Iraniyawa su fito kwansu da kwarkwatansu kan tituna a biranin kasar a ranar laraba 11 ga watan Fabrayru don gudanar da gagarumin zanga-zanga ta nuna goyon baya da kuma murna da cika shekaru 47 da nasarar juyin juya halin musulunci a kasar a shekara 1979.
Jagoran, a kiran nasa ya yi kira ga Iraniyawa su fito su kunyata makiya, su kuma nuna jajircewarsu a goyon baya ga JMI. Yace ranar 11 ga watan fabarayru rana ce ta nuna karfi da daukakan kasar Iran ga duniya musamman ga makiya kan cewa kasar Iran tana da cikekken yencin ta gudanar da al-amuran kasar ba tare da shishigin wasu kasashe ba.
Jagoran ya kara da cewa fitowar mutane kan tituna don nuna goyon bayansu ga JMI zai sa makiya su sake tunani a kan mummunan manufofinsu kan JMI da mutanen kasar.
Ya ce a ranar 22 ga watan Bahman shekara ta 1357 h.sh, wanda ta yi dai dai da 11 ga watan Fabrairun shekara ta 1979, kasar Iran ta sami yenci, kuma mutanen kasar sun kubutar da ita daga hannun manya-manyan kasashen duniya wadanda suka bautar da mutanen kasar kafin haka. Yace tun lokacin gwamnatin JMI tare da goyon bayan mutanen kasar suke gwagwarmaya da wadannan kasashen yamma don tabbatar da yencin da ta samu a shekara 1979.
Yace jerin gwano ko gaggamin bukukuwan samun nasara a ranar Larabawa mai zuwa gangami ne na nuna karfin mutanen kasar da kuma karfin JMI a gaban makiya, wanda zai sa su sau sauya ra’ayinsu dangane da ita.
Jagoran ya kammala cewa, tare da wannan fitar mikiya zasu ji kungiya su kuma jada baya daga mummunan manufofinsu kan kasar, idan ba haka ba zasu ci gaba da takalar kasar. Su kuma hana zaman lafiya a cikinta.
Masana sun bayyana cewa a bukukuwan cika shekaru 47 da nasarar juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran a ranar Laraba mai zuwa, Iraniyawa zasu nunawa makiya suna tare da gwamnatin JMI, wacce suka bayyana anniyarsu ta tumbuketa a fili. Musamman bayan sun gaza a yakin kwanaki 12 a cikin watan Yunin shekara ta 2025 da ta gabata. Da kuma ayyukan ta’addancin da ma’aikatansu suka haddasa a farkon wannan shekara wanda ya lakume rayukan mutane 3117.
Kafin haka a yankin kwanaki 12 a cikin wayan yunin da ya gabata Amuraka da HKI sun sun kashe mutanen kasar Iran kimani dubu guda, daga cikinsu har da manya-manyan kwamandojin sojojin kasar da kwararru masana fasahar makamashin nukliya da kuma mutane fararen hula, maza da mata da yara, wadanda basu san hawa ko sauka ba.
Don haka a ranar Laraban mai zuwa mutanen kasar Iran zasu nunawa makiya shirin farwa kasar da yaki ma ba zai kaisu ga samun nasara a kan JMI ba. Saboda Allah da kuma mutanen kasar suna goyon bayan gwamnatin kasar, kuma a shirye suke su bada duk abinda suka mallaka daga cikin har da rayukansu don kare gwamnatin kasar daga makiyanta.
A halin yanzu dai gwamnatin kasar Amurka ta kawo jiragen ruwan yakinta dauke da jiragen saman yaki, da nufin farwa kasar Iran da yaki, har sai ta kwace iko da shugabannin juyin juya halin msulunci a kasar.
Amurka da kasashen yamma dai suna goyon bayan HKI a kan kissan kiyashin da take ci gaba da yaki a kan falasdinawa a gaza tun ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023. Kuma ya zuwa yanzu sun kashe falasdinawa kimani 72,000 a gaza kadai. Kuma har yanzun suna ci gaba da kissansu. Da kuma neman duk wata hanya ta gidan bayansu a zirin gaza.
Dangane da halin da ake ciki a yankin dai, a lokacinda gwamnatin kasar Iran musamman jagoran juyin juya halin musulunci na kasar ya bayyana cewa duk wani yakin da kasar Amurka zata kaiwa kasar Iran a wannan karon, ba wai zata rama sai ta yi shiru ba. Sai dai a wannan karon yakin zai kasance ta yankin ne gaba daya. Yace ba su bar wani sansanin sojojin Amurka a yankin ba face sun kai masa hari. Sannan kasashen da suka bar Amurka ko HKI suka yi amfani da kasarsu ko sararin samaniyarsu don kaiwa kasar yaki, su ma ba zasu tsira ba.
Tare da wannan ne Amurka ta jinkirta kaiwa kasar Iran yaki ta kuma bukaci tattaunawa da ita. A ranar jumma’an da ta gabace ce aka gudanar da zagaye na farko na tattaunawa kan shirin Iran na makamashin Nukliya.