Moroko: Ambaliyar Ruwa Ta Sa An Dauke  fiye Da  Mutane 150,000  

Rahotannin da suke fitowa daga kasar Moroko sun ce ruwa kamar da bakin kwarya da yake sauka a yankunan arewacin kasar, ya sa an dauke mutanen da sun kai 150,000 zuwa wasu yankuna na daban. A garin Ould Ameur an rika yin kira ga mutane ta amsa amon masallaci da su gaggauta ficewa daga garin, […]

Jagoran Juyin Musulunci: Wajibi Ne Al’ummar Iran Su Sa Abokan Gaba Yanke Kauna

A jawabin da ya gabatar ga al’ummar Iran a yau Litinin, jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya ce; A kowace shekara al’ummar Iran suna bayyana girman matsayinsu a daidai lokacin da ake tuna zagayowar ranar cin nasarar juyin musulunci ta 22 ga watan Bahman na hijira shamshiyya, wanda ya yi daidai […]

Araqchi Ya Ce: Iran Ba Zata Taba Mika Wuya Ga Munanan Manufofi Ba

Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Iran ba zata taba mika kai ga barazana ko umarni ba A cikin wani sako kai tsaye kuma tabbatacce ga Amurka, Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa: Manufofin barazanar da tarin karfin sojoji ba su yi nasara ba, kuma ba za su yi nasara […]

Haramtacciyar Kasar Isra’ila Tana Kokarin Hana Cimma Duk Wata Yarjejjeniya Da Iran

Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta yi wa Trump gargaɗi kuma tana kokarin hana cimma duk wata yarjejeniya tsakanin Iran da Amurka Gwamnatin mamayar Isra’ila tana ƙoƙari sosai don dakile duk wata yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran wadda ba ta haɗa da shirin makami mai linzami na Iran ba, tana barazanar ɗaukar mataki ba tare da wani […]

Hamas ta yi watsi da bukatar mika makamai

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi watsi da kiraye kirayen mika makamai da kuma salon mika ragamar mulkin zirin ga hannun ‘yan kasashen ketare. Wani babban jami’i a kungiyar ya yi watsi da kiraye-kirayen yana mai adawa da bukatun Amurka da Isra’ila. Khaled Machaal, tsohon shugaban Hamas kuma darektan ofishin kungiyar na yanzu a […]

Iran : Muna kan tantance bukatun Amurka

Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ya yi Karin haske game da tattaunawar da ta wakana tsakankin kasar da Amurka a ranar Juma’a da ta gabata. Abbas Araghchi, ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran (IRI) tana tantance matsayin Amurka, kafin ya fayyace cewa tattaunawar, idan ta ci gaba, za ta mayar da hankali ne […]

Afirka ta Kudu Ta Janye Sojojinta Daga tawagar MONUSCO

Afirka ta Kudu ta sanar cewa za ta janye sojojinta kusan 700 da aka tura tare da tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD wato MONUSCO, a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo. Wannan shawarar, ta zo ne yayin da gabashin kasar ke ci gaba da fuskantar tashin hankali daga kungiyar M23 da kuma rikice-rikicen da suka ci […]

Aljeriya ta soke yarjejeniyar jiragen sama tsakaninta da UAE

Aljeriya ta soke yarjejeniyar jiragen sama tsakaninta da Hadaddiyar Daular Larabawa. Wannan matakin farko na zahiri da Algiers ta dauka kan Abu Dhabi ya zo ne a daidai lokacin da Aljeriya ke sukan Hadaddiyar Daular Larabawa tsawon shekaru kan shishigi a harkokin wasu kasahen yankin. A matakin farko da ta dauka na zahiri kan Hadaddiyar […]

Gaza : Yaran Falasdinawa 37 Isra’ila ta kashe tun farkon wannan shekara

Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya ruwaito cewa akalla yara 37 ne suka mutu tun farkon shekarar nan ta 2026 a hare-haren da Isra’ila ta kai a Zirin Gaza. Daraktan UNICEF a yankin na Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka Edouard Beigbeder, ya ce lamarin ya ci gaba da zama “mai […]