Sharhi Kan: Rikicin Watan Jenerun 2026 Da Watan Satumban 1978 A Iran, daya ne

Assalamu alikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na sharhin bayan labarai, shirimmu nay au zai magana a kan

Assalamu alikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na sharhin bayan labarai, shirimmu nay au zai magana a kan rikicin watan jenerun shekara da 2023 da ta watan satumban shekara 1978. Wanda ni tahir amin zan karanta

////..makonni kafin a gudanar da bukukuwan cika shekaru 47 da nasarar juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran, Amurka da HKI sun ingiza wasu ma’aikatansu yan ta’adda dauke da makamai sun kwace zanga-zangar limani wanda mutanen kasar Iran suke yi don kokawa gwamnatin kasar Iran halin da suke ciki na tabarbarewar tattalin arzikin kasar saboda takunkuman tattalin arzikin da kasashen yamma musamman Amurka suka dorawa kasar tun fiye da shekaru 40 da suka gabata. Wanda ya jawo faduwar darajar kudaden kasar.

Wadandan tashe tashen hankula wadanda suke nufin kifar da gwamnatin JMI sun yi sanadiyyar mutuwar mutane 3117 kamar yadda al-kaluman gwamnatin JMI suka tabbatar, amma kafafen yada labarai na makiya sun yi ta wasa da wannan addanin har suka kaishi kusa da dubu 60 don su halattawa ayayen gajansu farwa kasar Iran da yaki.

Amma idan mun dauko abinda ya faru a farkon watan jeneru na wannan shekara ta 2026 muka hada shi da abubuwan da suka faru a kasar Iran bayan nasarar juyin juya halin musulunci a nan Iran, muna iya fahintar ainihin abinda ya faru a cikin watan jeneru na wannan shekarar, da ace mun karanta shi shi kladai ba tare da komawa tarihi ba.

A cikin watan satumban shekara 1978 watanni kimani 5 da nasarar juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran wato a cikin watan Fabrayrun shekara ta 1979, zamu ga cewa tarihi ne ya maimaita kansa.

Saboda a lokacin da al-amura suka yi zafi a zamamin sarki sha Muhammad Riza, miliyoyin mutanen kasar Iran suka fara fitowa kan tituna a Tehran da kuma wasu birane a nan kasar Iran. Gwamnatin sarki sha ta kama doka ta bace a duk fadin kasar Iran ya kuma hana mutane fita kan tituna a kasar saboda murkushe zanga-zanga wacce take yin allawadai da sarki sha yake kuma goyon bayan Imam Khomaini (q) wanda daga baya ya kafa JMI.

Gwamnatin sarkin ta bada sanarwan kafa doka ta baci a cikin dare, don haka mafi yawan mutane basu san an kafa dokar ba sai suka fita kan titi a kusa da dandanlin Jale wanda ake kira maidane Shuhada a halin yanzu. Daga nan Jami’an tsaro ko kuma sojojin sarki sha suka bude masu wata, ba don tarwatsasu ba sai dai don kashe su.

Banda haka wasu labarai sun bayyana cewa Gwamnatin HKI a lokacin ta aike da sojoji zuwa kasar Iran inda suka zo da sabbin makamai, kuma na zamani don taimakawa gwamnatin sarkin murkushe zanga zangar.

Da farko kafafen yada labarai na cikin gida sun fara cewa ai mutane 55 ne kawai aka kashe, daga baya suka daga shi zuwa 95. Amma kafafen yada labarai na kasashen yamma wadanda suka ganewa idanunsu abinda ya faru kuma suke da hotonan abinda ya faru sun fara bada rahoton cewa an kashe daruruwa don kare gwamnatin sarkin daga bacin suna.

Sannan jami’an diblomasiyya wadanda suka ganewa kansu su ma sun san cewa an kashe dubban mutane. Wani jakadan daya daga cikin kasashen yamma a nan Tehran  ya bada sanarwan cewa ya je makabartan Beheshti Zahra ya ga lamba 1700 da wani abu na butane da aka bisne, wadanda hukumar savak ta amince da cewa an kashe su.

Ganin yawan mutanen da suka kashe  mai data hankali sai sai suka yi ta boye adadin. Sun kuma fara gabatar da dalilai na kashe mautanen Iran masu yawa kamar haka. Wasu su ce an kashesu ne don murkushe fitina a kasar don haka ya halatta.

Shugaban kasar Amurka a lokacinb Jimi Carther, yana camp Devid yana kuma shirin ganin HKI da Masar sun rattaba hannu kan shirin Camp Devid, don haka ya kira sarki Muhammad Reza yana nuna goyon bayansa tare da da fada masa kada ya damu.

Don haka idan an kwatanta abinda ya faru a cikin watan Jenerun shekara ta 2026, inda a wannan karon ma, wadanda suka kashe Iraniyawa a cikin watan Satumban shekara 1978 sune suka kawo yan ta’adda dauki da makamai suka tsarawa wadanda suke aiki da su a cikin Iraniyawa abinda zasu yi, na kashe mutanen Iran, harm un ji wani Jami’in Mosad yana cewa suna son su ga an kashe mutane akalla 800,000. Wanda hakan zai share masu hanya na farfa ganda, a duniya na aiwatar da aikin soje a kasar Iran da sunan kubutar da mutanen kasar daga hannun shuwagabannin addini na kasar.

Da wannan dalilin ne sai kafafen yada labarai na wadannan kasashen musamman Iran Internationan suke daga al-kaluman yawan mutanen da aka kashe a rikicin watan watan Jeneru na wannan shekara daga adadin da gwamnatin kasar Iran ta bayar na 3117 zuwa har fiye da dubu 50 don halattawa iyayen gidansu farwa kasar Iran da yayi. Da sunan tana kashe mutanen kasar.

Sai dai tunda an yi ta nanata rikicie rikice a kasar Iran tun bayan nasarar juyin juya halin muslunci a kasar Iran, wanda ya hada da na wanda Munafukin shugaban kasa Banisadar ya haddasa, wanda kuma saboda hikimar Imam  Khomaini (s) ba’a zubar da jinin mutane masu yawa, sai kuma yakin shekaru 8 wanda Saddam Hussain tare da taimakon dukkan manya-manyan kasashen duniya a lokacin suke goyon bayansa ya dorawa kasar.

Sai kuma bayan yakin, an yi tashe tashen hankula da dama wadanda wadannan kasashe suka hassa, akwai na bayan zaben shekara ta 20009, na kara farashin man fetur, da mutuwar Mahsa Amini da yakin kwanaki 12, da kuma na watan jenerun shekara ta 2026 da muke ciki.

A ko wannen wadannan kasashe sune bayan tashe tashen hankulan, kuma manufa guda ce wato kifar da JMI. Sannan da alamun an zo marhala ta karshe bayan da Amurka ta  kawo makamanta a kusa da JMI, tare da manufar kifar da gwamnatin kasar da karfin tsiya ko ta mika kai. Amma da alamun sun dan dan zaki ya girma.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments