Senegal: Kotun Tsarin Mulki Ta Yi Watsi Da Kudurin Majalisa Na Rage Karfin Shugaban Kasa

Kotun tsarin Mulki ta kasar Senegal ta yi watsi da wani kuduri na majalisar dokokin kasar wanda yake nufin kayyade karfin ofishin shugaban kasar da

Kotun tsarin Mulki ta kasar Senegal ta yi watsi da wani kuduri na majalisar dokokin kasar wanda yake nufin kayyade karfin ofishin shugaban kasar da kuma karfafa majalisar dokoki.

A jiya Alhamis ne dai kotun tsarin mulkin da ita ce cibiyar shari’a mafi karfi a kasar Senegal ta soke kudurin da majalisar dokokin kasar ta yi na rage karfin shugaban kasa da karfafa majalisar dokoki.

Wancan matakin na majalisar dokokin kasar dai an yi shi ne a tsakiyar sabanin da ake yi a tsakanin shugaban kasa Faye da tsohon fira minista kuma shugaban majalisar dokoki na yanzu Usaman sonko.

Shugaban kasar ne dai ya gabatarwa da kotun tsarin mulkin matakin da majalisar dokoki ta dauka wacce ya bayyana a matsayin mai cin karo da tsarin Mulki.

A karkashin kudurin majalisar an hana shugaban kasa zama shugaban jam’iyyarsa ko shugaban jam’iyyun hadaka. Haka nan kuma ya bai wa majalisar dokoki karfin gudanar da bincike.

A halin yanzu dai Sonko shi ne yake jagorantar majalisar dokokin kasar da ta yi wannan kuduri, kuma shi ne shugaban jam’iyyar “Pastef” mai Mulki.

A makon da shude ne dai Faye ya sanar da cewa zai kafa tashi sabuwar jam’iyyar siyasa.

Wannan sabanin a tsakanin bangarorin biyu ya kara kamari ne adaidai lokacin da kae Shirin gudanar da zabukan kananan hukumomi a cikin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted