Abbas Araqchi Ministan harkokin wajen kasar iran ya isa kasar oman a yau tare da tawagar jamai’an diplomasiya dake rufa masa baya domin tattaunawa da mahukumtan kasar kan mashigar Hurmuz da kuma dangantar dake tsakaninsu da ma irin ci gaba da aka samu a yankin baki daya
Araqchi da tawagarsa sun samu kyakkyawar tarba a hukumance bayan isarsa kasar ta Oman inda ake saran a zaiyarar za’a ci gaba da tattaunawa tsakanin Tehran da Muskat kan abin da ya shafi harkokin sufurin teku da kuma yin hadin guiwa da tabbatar da tsaro a fadin yanki
kakakin ma’aikatar harkokin wajen iran esma’ila baqai yayi bayani game da ziyarar kuma yace karkashin yarjejeniyar da aka cimma, iran tana aiki da nauyin dake kanta na taimakawa wajen ganin an samar da tsari mai kyau a mashigar Hurmuz da ya hada da yin hidima ga jiragen ruwa na kasuwanci
wannan ziyara tana zuwa ne bayan tawagar kwararrru ta kasar iran karkashin jagorancin mataimakin ministan harkokin wajen iran kazeem Garibabadi ya tattauna a ranar 1 ga watan yuli da masu shiga tsakanin na kasashen Qatar da Pakistan na irin ci gaban da aka samu na aiwatar da yarjejeniyar Islamabad da aka sanyawa hannu ta kawo karshen yaki