Mutum miliyan 43 ne suka halarci jana’izar Shahid Ayatollah Khamenei a Iran da Iraki

Hukumomi a Iran sun kiyasta cewa sama da mutane miliyan 43 ne suka halarci jana’izar tsohon jagoran juyin juya halin musulinci na kasar a Iran

Hukumomi a Iran sun kiyasta cewa sama da mutane miliyan 43 ne suka halarci jana’izar tsohon jagoran juyin juya halin musulinci na kasar a Iran da Iraki.

An tattara alkalumman ne daga majiyoyi masu zaman kansu da na gwamnati da dama, wadanda suka tabbatar da cewa tsakanin mutane miliyan 41 zuwa 43 ne suka halarci wadannan tarurukan tarihi.

Wadannan alkaluma sun dogara ne akan hadakar bayanai masu karfi, wadanda suka hada da adadin fasinjojin sufuri na jama’a zuwa da kuma dawowa daga wuraren tarurukan, da bayanan da aka samu ta hanyar sadarwa ta wayar hannu a muhimman wurare kamar babban masalacin Tehran, da manyan hanyoyin tattaki, a Qom, da Mashhad.

Hakan ya nuna cewa shi ne mafi girman tarurukan jana’iza da aka taba gani a duniya, a cewar wani rahoto.

An gudanar da bukukuwan bankwana da jana’iza na kwanaki shida ga shahidin a birane biyar – Tehran, Qom, Najaf, Karbala, da Mashhad – kuma sun jawo dimbin jama’a, in ji kamfanin dillancin labarai na Fars na Iran.

An gudanar da bukukuwan tsawon kwanaki uku a Tehran, ciki har da kwanaki biyu na zaman makoki na kasa a babban masallacin Musalla da kuma kwana daya da aka kebe na zazagayawa da gawarsa.  

jami’an Iran da hukumomin da abin ya shafa sun jaddada cewa wannan babban taron ya zarce dukkan tarurrukan da aka yi a wannan karni.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted