Isra’ila Ta Hana Babban Muftin Yankin Falasdinu Shiga Masallacin Kudus Kafin Daga Bisani Ta Kama Shi

rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin yahudawan sahyuniya sun hana babban muftin yankin falasdinu shiga masallacin kudus na tsawon makon guda bayan ta kama shi, a

rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin yahudawan sahyuniya sun hana babban muftin yankin falasdinu shiga masallacin kudus na tsawon makon guda bayan ta kama shi, a wani mataki da ta fara dauka kan fitattun malaman addini a yankin falasdinu.

Isra’ila ta kama shaikh mohammad Hussain a ranar jumaa bayan da ya kammala huduba a masallacin kudus kafin daga baya su sake shi kuma suka hanashi shiga masallacin kudus na tsawon mako daya.

Sai dai isra’ila ta ce wannan ba shi ne karon farko da ta dauki wannan mataki kan Hussain ba ta bayyana cewa wani bangare ne irin mataken da take dauka na takurawa shuwagabannin addini a yankin falasdinu

A farkon wannan watan ma gwamnatin isra’ila ta yi tambayoyi da kuma kuntatawa shaikh Ekrima Sabri malamin da ya dauki lokaci yana wa’azi a masallacin kudus kuma tsohon mufti na birnin Qudus sun yi masa tambayoyi akai akai da kuma hana shi shiga yankin a yan shekarun nan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted