Sakacin Amurka akan bayannan sirri ya sanya ta kai hari kan makarantar Minab (CNN)

Wani rahoto da tashar CNN ta Amurka ta fitar ya nuna cewa, manyan kwamandojin sojojin Amurka sun yi sakaci da gargadin da ke cikin bayanan

Wani rahoto da tashar CNN ta Amurka ta fitar ya nuna cewa, manyan kwamandojin sojojin Amurka sun yi sakaci da gargadin da ke cikin bayanan sirri da aka basu kan wuraren da aka kai wa hari a Iran cewa sun tsufa a tantance su kafin a amince da kai hare-hare kan Iran, wanda daya daga cikinsu ya afka wa wata makarantar firamare a Minab, a kudancin kasar.

A cewar rahoton na CNN, bayyana da aka saka a cikin tsarin kai hari na Pentagon a Iran sun yi gargadin cewa ya kamata a sake duba bayanan sirri kafin a amince da wuraren a matsayin wuraren da za a kai hari.

Duk da haka manyan jami’ai sun ba da izinin, bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya amince fara kai harin.

A cewar rahoton, wannan ya taimaka wajen kai hari a Makarantar Firamare ta Shajareh Tayyebeh da ke birnin Minab na Iran a ranar 28 ga Fabrairu, ranar farko ta kai harin Amurka da Isra’ila kan Iran.

Hukumar tsaron Amurka ta Pentagon ta ce ta bude bincike jim kadan bayan wannan mummunan harin, amma watanni da dama bayan haka, har yanzu ba a fitar da sakamakon bincikenta ba. Wani jami’in Fadar White House ya shaida wa CNN cewa “wannan binciken har yanzu yana ci gaba.”

Harin na Minab ya yi ajalin mutane 168, galibi yara ‘yan shekara 7 zuwa 12, wanda hakan ya sanya ya zama daya daga cikin munanan abubuwan da suka faru da suka haifar da mutuwar fararen hula a tarihin sojojin Amurka na baya-bayan nan.

A cewar hukumomi, wannan makarantar firamare ta ‘yan mata mai hawa biyu an kai hari sau uku da makamai masu linzami na Tomahawk.

Da yake jawabi a gaban Majalisar Kare Hakkin Dan Adam ta MDD a watan Maris, Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya kira harin da “tashin hankali da akayi da gangan.”

Jakadan Iran a MDD, Amir Saeed Iravani, shi ma ya yi watsi da duk wani ra’ayi da ke nuna cewa harin kuskure ne, inda ya shaida wa Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a watan Yuni cewa ya kamata a hukunta Amurka kan “mummunan laifin” da ta aikata a makarantar ta Minab.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted