Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Gargadi Amurka Game Da Ci Gaba Da Ke ta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta

 a cikin wani bayani da ya wallafa a cikin shafinsa na X ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi yace yarjejeniyar da aka cimma za

 a cikin wani bayani da ya wallafa a cikin shafinsa na X ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi yace yarjejeniyar da aka cimma za tayi nasara ne idan dukkan bangarorin biyu suka yi aiki da shi, kana ya gargadi Amurka game da ci gaba da keta yarjejeniyar dakarar da bude wuta da kasar Pakistan ta shiga tsakani.

a ranar 7 ga watan yuli Amurka ta kaddamar da hari a wurare 80  har da naurar tsaro a kasar iran abin da ta kira mayar da martani kan matakin da Tehran ta dauka kan jiragen ruwanta a mashigar Hurmuz inda babbar cibiyar sojin Amurka ta bayyanashi a matsayin keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma.

sai dai dakarun kare juyin musulunci na iran sun mayar da martani kan wurare soji guda 85 na Amurka a kasashen Bahrain da Kuwait, inda shugaban Amurka Donald Trump ya sanar a ranar juma’a cewa jarjejeniyar da aka kulla ta mutu.

a jiya jumaa kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Esmail Baqai ya gargadi washington cewa idan ta sake keta yarjejeniyar da aka cimma a ranar 17 ga watan yuni za ta dauki matakin da ya dace.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted