Kwamandan Sojojin Iran, Manjo Janar Amir Hatami, ya yaba wa al’ummar kasar kan halartar jana’izar tsohon Jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar da ya yi shahada, yana mai cewa tarurukan sun aika sako bayyananne ga makiya, yana mai nuna cewa hanyar da Ayatollah Seyyed Ali Khamenei ya kafa za ta ci gaba da wanzuwa da karfi.
Ya yi wadannan kalaman ne a cikin wani sako ga Iraniyawa jiya Juma’a, ranar da aka binne Jagoran a birnin Mashhad mai tsarki, bayan jana’izar da ta samu halartar miliyoyin mutane a Iran da Iraki.
Ya bayyana cewa fitowar Iraniyawa dafifi, da Musulmai a wurin jana’izar shaida ce mai girma a tsakanin al’umma.
“Hanya da Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na Iran ya shimfida kamar mabubbugar ruwa ce mai gudana wadda za ta ci gaba da gudana; hanya ce da aka kafa a kan ginshikin gaskiya, adalci, da juriya wadda babu wani makirci ko shirin makiyi da zai iya rushe ta in ji shi.
Janar Hatami ya kuma Ya kuma gode wa ‘yan sanda, jami’an tsaro, da na soji na Iran, da kuma ma’aikatan lafiya, wadanda suka ba da gudummawa wajen gudanar da tarurukan jana’izar cikin kwanciyar hankali.
Shi ma Shugaban kasar ta Iran Massoud Pezeshkian ya gode wa gwamnatin Iraki da al’ummarta bisa shirya jana’izar jagoran.
“Mutanen Iran ba za su taba mantawa da wadannan abubuwan tarihi na hadin kai da goyon baya ba,” in ji shi.
A cikin wani sako da aka wallafa a harshen Larabci a dandalin sada zumunta na X a ranar Juma’a, Pezeshkian ya bayyana godiyarsa ga shugaban Iraki Nizar Amidi, Fira Minista Ali al-Zaidi, jami’an Iraki, hukumomin addini, da kuma al’ummar Iraki saboda karbar gawar Jagoran Shahhid, Ayatollah Seyyed Ali Khamenei.
Sakonsa ya zo ne bayan da masu shirya taron a Iraki suka sanar da cewa sama da masu makoki miliyan 10 sun halarci jana’izar da aka gudanar ranar Laraba a biranen Najaf da Karbala masu tsarki.