Iran ta yi watsi da ikirarin cewa Tehran ta nemi tattaunawa da Amurka

Iran ta yi watsi da ikirarin cewa Tehran ta nemi tattaunawa da Amurka. Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya yi watsi da ikirarin, yana mai

Iran ta yi watsi da ikirarin cewa Tehran ta nemi tattaunawa da Amurka.

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya yi watsi da ikirarin, yana mai gargadin cewa saba yarjejeniyar fahimtar juna da Washington ta yi a ranar 17 ga Yuni, kuma Iran za ta maida martini daidai wadaida.

Esmaeil Baqaei, a wata hira da IRIB’s News Network, ya mayar da martani ga ikirarin jami’an Amurka game da tattaunawa da tsagaita wuta.

“Ba mu nemi tattaunawa da Amurka ba,” in ji shi, yana mai kara da cewa Iran, duk da haka, ta amince da bukatar wani mai shiga tsakani na yankin na ziyartar Tehran da tattauna halin da ake ciki, tare da musayar ra’ayoyi a lokacin tattaunawa a Mashhad a ranar Juma’a.

Mista Baqae’i ya jaddada cewa “saba wa alkawuran Amurka dabi’a ce,” yana mai nuni da cewa a shekarar 2018, Amurka ta janye daga yarjejeniyar nukiliya ta 2015.

Ya lura cewa Amurka ta saba wa sassa daban-daban na yarjejeniyar fahimtar juna mai maki 14 a cikin kwanaki 22 da suka gabata tun bayan sanya hannu kan yarjejeniyar.

Ya ambaci hare-haren Amurka a ranar Laraba da Alhamis a matsayin babban keta sassa na farko da na biyu na yarjejeniyar, wadanda ke kira da a kawo karshen ayyukan soji.

Ya kuma yi Allah wadai da soke lasisin sayar da mai na Iran da kuma sanya sabbin takunkumi a matsayin karin keta haddi na dage takunkumi.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran, ya jaddada cewa Iran ta bayyana karara cewa ba za ta aiwatar da wani alkawari ba tare da daukar matakin mayar da martani ba.

“Idan daya bangaren ya karya alkawarinsa, Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta dauki matakin da ya dace.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted