A wani sabon rahoton da Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar ya nuna cewa akalla mata da ƴan mata miliyan daya ne suka fuskanci katsewar tallafin jin kai a bara, saboda dakatar da bayar da agaji da kasashe da hukumomi da dama su ka yi.
har ila yau Rahoton ya yi duba kan halin da mata ke cika a sassan duniya, ya ce kusan 9 cikin kowace kungiyoyin dake tallafawa mata 10, basa iya cimma muradunsu, saboda yadda ake samun karuwar mata da ke bukatar tallafi tun daga watan Janairun 2025.
Gwamnatin shugaba Donald Trump ta yanke bayar da tallafi na dala biliyoyin a shekarar nan, yayin da sauran hukumomi da ke tallafawar, suka rage bayar wa saboda matsalar da suke fuskanta kan kasafin kudi musamman a fannin tsaro.
Rahotan ya ce mata da ƴan mata miliyan 120 ne ke bukatar tallafin jin kai da kariya a sassan duniya, to sai dai kashi 40 cikin 100 na kungiyoyin tallafawa mata 855 a kasashen Afghanistan da Congo da Haiti, na fuskantar barazanar dakatar da ayyukansu na wucin gadi ko dindindin nan da badi saboda rashin kudaden tafiyar da ayyukansu.