A ci gaba da hare-haren da isra’ila ke kai wa a yankunan kudancin labanon, ta kashe wani mutum guda tare da jikkata wasu da dama, kuma tana ci gaba da kai harin ne duk da shirye-shiryen da ake yi na fara aiwatar da yarjejeniyar da aka kulla tsakanin berut da telaviv da kasar Amurka ta shiga tsakani.
harin da isra’ila ta kai ya fada akan wani mutum dake kan babur a titin al-doha dake garin kfrrumman a yankin nabatiya a jiya da yamma, inda wani matashi yayi shahada nan take kamar yadda hukumomi suka bayyana.
haka zalika sojojin isra’ila sun dauki matakin rushe – rushe a kan iyakar ta da garin khiam dake yankin marjaiyun kuma sun kewaye wajen kuma suka sanya wasu ababen fashewa masu karfi da suka tarwaste a cikin dare hare-haren da isra’ila ta kai a ranar 2 ga watan maris kan kasar labanon yayi sanadiyar mutuwar mutane 4300 tare da jikkata 12200 kamar yadda rahoton da gwamnatin labanon ta fitar, kuma ya tilastawa sama da mutane miliyan daya barin gidajensu.