Search
Close this search box.

Karon Farko Saudiyya Ta Nada Jakada A Siriya Tun Bayan 2012

Saudiyya ta nada jakadanta a Syria a karon farko tun bayan da kasar ta rufe ofishin jakadancinta a Damascus a shekara ta 2012. Kamfanin dillancin

Saudiyya ta nada jakadanta a Syria a karon farko tun bayan da kasar ta rufe ofishin jakadancinta a Damascus a shekara ta 2012.

Kamfanin dillancin labaran Saudiyya SPA ya bayyana a ranar Lahadin cewa, sabon jakadan Riyadh a Syria zai kasance Faisal al-Mujfel.

Rahoton ya ambato sabon jakadan na Saudiyyar yana fatan yin aiki da muradun masarautar tare da karfafa dankon zumunci tsakanin kasashen biyu.

Tun a farkon wannan shekara ne Saudiyya ta bude ofishin jakadancinta a kasar Siriya tare da gudanar da harkokinta bayan da gwamnatin Siriya ta bude ofishin jakadancinta na Riyadh a bara tare da nada sabon jakada a watan Disamba.

Sake kulla alaka tsakanin Riyadh da Damascus wani sabon ci gaba ne a cikin jerin matakan da kasashen Larabawa yankin ke dauka na dinke baraka da Syria.

Matakin da kasashen Larabawa suka dauka na sake kulla alaka da kasar Siriya ya zo ne bayan samun nasarar kwato yankuna da dama na kasar daga hannun ‘yan ta’addar da ke samun tallafi daga kasashen waje.

A farkon watan Janairu ne UAE ta aike da jakadanta na farko zuwa Syria bayan shekaru 13, bayan da aka dawo da huldar jakadanci tsakanin kasashen biyu.

A watan Mayun shekarar 2022, ne kungiyar kasashen Larabawa mai mambobi 22, ta amince ta maido da kasar Syria mamba a cikinta, wanda ya kawo karshen dakatarwar da aka yi na tsawon shekaru 12.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments