Search
Close this search box.

Saudiyya Da Sudan Sun Tattauna Batun Zaman Jeddah Don Dakatar Da Yaki A Sudan

Kasashen Sudan da Saudiyya sun tattaunawa kan batun sake komawa zaman birnin Jeddah don neman hanyar dakatar da yakin Sudan Shugaban majalisar gudanar da Mulki

Kasashen Sudan da Saudiyya sun tattaunawa kan batun sake komawa zaman birnin Jeddah don neman hanyar dakatar da yakin Sudan

Shugaban majalisar gudanar da Mulki a Sudan Janar Abdul Fattah Al-Burhan ya tattauna da Walid bin Abdulkarim Al-Kheraiji mataimakin ministan harkokin wajen Saudiyya kan batun dawo da zaman tattaunawan Jeddah da nufin ganin an dakatar da yakin da ake yi tsakanin sojojin Sudan da Rundunar Dakarun Kai Daukin Gaggawa ta Rapid Support Forces.

A sanarwar da Majalisar Gudanar da Mulkin Sudan ta fitar ta ce: Al-Burhan ya gana da Al-Kheraiji, wanda ya isa birnin Port Sudan da ke gabashin Sudan a wata ziyarar aiki da ba a bayyana ba.

Sanarwar ta ambato karamin sakatare na ma’aikatar harkokin wajen Sudan Hussein Awad yana cewa tattaunawar ta shafi kiran dawo da dandalin birnin Jeddah da ke shiga tsakanin bangarorin da suke fada da juna a Sudan.

Awad ya kara da cewa: Al-Burhan ya jaddada burin kasar Sudan na ganin dandalin Jeddah ya samu nasara a matsayin tushen neman zaman lafiya a Sudan, yana mai jaddada wajabcin aiwatar da abin da aka amince da shi a watan Mayun shekarar 2023.

Ya fayyace cewa: Zaman taron ya kuma tattauna kan muhimmancin fadada tushen masu shiga tsakani a zaman tattaunawan birnin Jeddah, kuma shugaban majalisar gudanar da mulkin Sudan ya bayyana adawarsa da kasancewar duk wani bangare da ke goyon bayan mayakan Dakarun Kai Daukin Gaggawa na Rapid Support Forces da gwamnatin Sudan take daukansu a matsayin ‘yan tawaye a matsayin masu shiga tsakani.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments