Search
Close this search box.

Sakon Jagora Ga Mahajjatan Bana : Dole Ne Kin Jinin Amurka Da Mulkin ‘Yan Sahayoniya Ya Yadu A Duniya

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya kira ga musulmi da su ba da cikakken goyon baya ‘yan gwagwarmayar Falastinawa

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya kira ga musulmi da su ba da cikakken goyon baya ‘yan gwagwarmayar Falastinawa da al’ummarta ta kowace hanya.

A cikin sakonsa na aikin Hajji na shekara-shekara, Jagoran ya yi kira ga miliyoyin alhazai daga kasashen duniya dake aikin hajji a Makka, da su nuna rashin amincewarsu da gwamnatin sahyoniya da magoya bayanta, musamman Amurka, a aikace ba wai da fatar baki ba.

Ayatullah Khamenei ya tabo abubuwan da suka faru a zirin Gaza, wadanda ya ce basu taba faruwa ba a tarihin wannan zamani.

Ayatullah Khamenei ya kara da cewa, tsayin daka na Falasdinawa, wadanda ake zalunta a Gaza dole ne a ba su cikakken goyon baya ta kowace fuska.

Ga cikakken sakon da Jagoran ya aikewa Alhazan 2024:

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin kai

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da aminci su kara tabbata ga fiyayyen halitta, shugabanmu Muhammadu al-Mustafa, da alayensa tsarkaka, da sahabbansa zababbu da wadanda suka bi su da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.

Wannan kira na Ibrahim mai jan hankali, wanda bisa ga umarnin Allah ya yi kira ga dukkan bil’adama a kowane zamani zuwa dakin Ka’aba a lokacin aikin Hajji, ya sake janyo hankulan dimbin al’ummar musulmi daga sassan duniya zuwa wannan waje.

Idan mutum ya yi la’akari da wannan gagarumin taro mai hade da ibadar Hajji, su ne abin da zai sanyaya zuciya da kuma kara kwarin gwiwa ga musulmi, tare da zama abin tsoratarwa da firgita ga makiya da masu mugun nufi.

Alkur’ani ya gabatar da aikin Hajji a matsayin babbar ibada, data hada da zikiri (ambaton Allah), rashin girman kai.

‘Yan’uwa, a matsayinku na mahajjata masu gudanar da aikin Hajji, a halin yanzu kuna wurin da za ku iya aiwatar da wadannan ayyukan na gaskiya.

Wannan shi ne muhimmin abin tunawa na hakikanin tafiyar ku Hajji.

A wannan shekarar, lamarin makiya ya fi daukan hankali fiye da ko wane lokaci..

Masifun da ke faruwa a Gaza, wadanda ba su misaltuwa a tarihinmu na wannan zamani, a yadda gwamnatin sahyoniya maras tausayi ta jajirce wajen aikata ayyuka na rashin tausayi da zalinci, basu cancanci wani tausayi ba.

Tilas ne a ci gaba da yin watsi da mushrikai ko bayan aikin Hajji, lamarin ya yadu zuwa dukkan kasashen musulmi da garuruwan duniya.

Wannan watsi da gwamnatin Sahayoniya da magoya bayanta, musamman gwamnatin Amurka, wajibi ne a dakile ayyukan su.

Dole ne a ba al’ummar ffalasdinu cikakken goyon baya ta kowace hanya.

Ina rokon Allah Ya ba su cikakkar nasara kuma cikin gaggawa.

Kuma ga ku alhazai ina yi muku addu’a, Allah ya karbi aikin Hajjin ku.

Addu’ar Imam Mahdi (Rai Na Ya Kasance Fansasa) ta game da ku..

Tare da gaisuwata da rahmar Allah ta tabbata a gare ku!

4 Dhul-Hajjah 1445

11 Yuni, 2024

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments