Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehran ya bayyana cewa: Yarjejeniyar fahimtar juna da aka cimma ta dogara ne akan ka’idar sadaukarwa ga alƙawari
Limamin da ya jagorancin sallar Juma’a a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran Hujjatul -Islam Muhammad Hassan Abu Turabi Fard, ya jaddada cewa: Tsarin yarjejeniyar fahimtar juna (MOU) tsakanin Iran da Amurka ya dogara ne akan ka’idar “sadaukar da kai ga alkawari,” kuma Iran ta bayyana karara cewa ba za ta bar Amurka, a kowane hali, ta tsoma baki a harkokin mashigar ruwan Hormuz ba.
A cewar kamfanin dillancin labarai na Jamhuriyar Musulunci (IRNA), Hujjatul-Islam Abu Turabi Fard ya bayyana cewa: Yarjejeniyar ba ta dogara ne akan amincewa da gwamnatin Amurka ba, yana mai karawa da cewa: Tsarin yarjejeniyar ya dogara ne akan ka’idar “sadaukar da kai ga alkawari,” kuma Iran ta bayyana karara cewa: Ba za ta bari Amurka ta tsoma baki a harkokin mashigar ruwan Hormuz ba.
Kamfanin dillancin labaran na “IRNA” ya kara da cewa: Hujjatul-Islam Abu Turabi Fard, yana magana daga kan mumbarin sallar Juma’a a Tehran a yau, yana mai nuni da karya yarjejeniyar da shugabannin Amurka suka yi, ya tabbatar da cewa gwamnatin Amurka, ta hanyar ayyukanta na gefe da hare-haren ta’addanci, ta karya ruhin yarjejeniyar kuma ta aikata laifukan yaki a fili.