Jaridar “Ra’ayul-Yaum” ta buga wani labari wanda ya kunshi cewa; Da akwai kasashe 43 da su ka halarci taron da aka yi a birnin Riyadh akan kafa kawance na sojojin ruwa daga cikinsu har da UAE, sai dai kasashen da su ka rattaba hannu akan bayanin da aka fitar ba su wuce 14 ba.
Daga cikin kasashen da ba su rattaba hannu ba da akwai Amurka, Birtaniya, Faransa, Italiya da Indiya. Sai kuma kasashen China, UAE da kuma Oman.
Bugu da kari, jaridar ta ce wannan kawancen ba shi da wani muhimmanci bisa la’akari da kasashen da su ka kaucewa rattaba hannu akan bayanin bayan taron na Riyadh.
Haka nan kuma kasar UAE ta yi suka akan wannan kawancen na Saudiyya, wanda Saudiyya ta mayar da martani ta bakin tsohon shugaban hukumar al’adu da ilimi na kungiyar “Icesco” Abdulaziz Bin Usman al-tuwaijari, yana cewa:
“Wanda duk yake cin amanar kafa kawance, bai cancanta ya shiga cikin wani kawance ba.” Haka nan kuma ya kara da cewa: Tsaron kasar Saudiyya, jan layi ne.”
Gabanin kwanaki 10, an yi musayar yabon juna tsakanin ministan sadarwa na Saudiyya Salman al-Dusari, da kuma shugaban hukumar watsa labaru ta UAE Abdullahi Bin Muhammad ali-Hamid da su ka bayyana cewa alaka a tsakanin kasashen biyu tana da karfi, kuma bai kamata kafafen watsa labaru su rika kokari bata ta ba.
A watanni kadan da su ka gabata, kasashen biyu sun yi fada da juna a kasar Yemen, inda Saudiyya ta kori wadanda UAE take goyon bayan daga gundumar Hadhara-maut mai makwabtaka da Saudiyya, kuma mai muhimmanci ta fuskar tattalin arziki.