Ruwa Ya Ci Rayukan Mutane 14 A Habasha

Kamfanin dillancin labarun AFP ya nakalto cewa a kalla mutane 14 ne su ka mutu yayin da wasu 5 su ka jikkata a wata cibiyar
Ambaliyar ruwa

 Kamfanin dillancin labarun AFP ya nakalto cewa a kalla mutane 14 ne su ka mutu yayin da wasu 5 su ka jikkata a wata cibiyar addini a Arewacin gundunar Amhara ta kasar Habasha.

Kasar ta Habasha dai tana fuskantar ruwa kamar da bakin kwarya a cikin kwanakin nan na damina da ta fara tun a cikin watan Yuni, za kuma ta cigaba zuwa Satumba.

Ruwan saman dai ya haddasa zaizayar kasa ne a yanki “Sela Dingay’ mai nisan kilo mita 200 daga babban birnin kasar Addis Ababa.

Malamin addini a yankin Megabe Hadis Neka Ababu ya ce; da safiyar Litinin din nan ne dai aka sami afkuwar zaizayar kasar, bayan aka kwashe daren Lahadi ana ruwa da cida mai karfi.

Makamkon ruwan ya yi sanadiyyar gangarowar duwatsu akan cibiyar addinin ta “Tsadkane Mariam” da hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 14 masu ibada a ciki nan take. Sai kuma wasu 3 da su ka jikkata, amma tuni an dauke su zuwa asibitin “Debre Birhan” saboda karbar magani.

Kasar ta Habasha dai tana fuskantar irin wannan yanayi na ambaliyar ruwa wanda baya rasa alaka da dumamar yanayin duniya.

A  watan Yuli na shekarar 2024 mutane 257 su ka kwanta dama sanadiyyar zaizayar kasa, sai kuma wasu 80 su ma su ka rasu  a watan Maris a wannan gundumar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted