Rundunar tsaron juyin juya halin Musulunci ta kai hari da makami mai linzami a matsayin ramuwar gayya kan harin da aka kai wa daya daga cikin wuraren hakar mai na Iran
Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci ta (IRGC) ta sanar a wata sanarwa a hukumance cewa: Dakarunta masu kula da makamai masu linzami sun mayar da martani kan harin da ‘yan Sahayoniya da Amurka suka kai kan daya daga cikin cibiyoyin man fetur na Iran. Sanarwar ta nuna cewa mayakan Rundunar Tsaron Jiragen Sama ta IRGC sun kai harin makami mai linzami kan wuri makamancin haka a Haifa a Isra’ila.
Rundunar Tsaron IRGC ta fitar da wata sanarwa a ranar Litinin, 8 ga Yuni, wadda ta ce: “Da taimakon Allah, mayakan Rundunar Tsaron Jiragen Sama ta IRGC sun kai harin makami mai linzami kan cibiyar man fetur a Haifa, a matsayin mayar da martani ga harin da abokan gaban ‘Yan Sahayoniyya da Amurka suka kai kan daya daga cikin wuraren man fetur kasarta.”
Sanarwar IRGC ta kara jaddada gargadinta, tana mai cewa: “Ta hanyar kai hari kan wuraren fararen hula da wuraren mai, makiya ‘yan Sahayoniya sun fara wani mummunan wasa wanda zai shafi dukkan wuraren samar da makamashi a yankin. Amurka, a matsayin babbar mai tayar da hankali, tana da cikakken alhakin illolin da hakan zai yi wa tattalin arzikin duniya .”