Rikicin Sudan Ya Kara Tarwatsa Al’umma Da Bullar Cututtuka Da Suke Kisa

Kimanin mutane 1,000 ne suka mutu sakamakon yunwa da cututtuka a yankin Darfur da ke yammacin kasar Sudan Rahotonni sun bayyana cewa: Guguwar kaura ta

Kimanin mutane 1,000 ne suka mutu sakamakon yunwa da cututtuka a yankin Darfur da ke yammacin kasar Sudan

Rahotonni sun bayyana cewa: Guguwar kaura ta sake kadawa a Sudan, yayin da sama da mutane 50,000 suka tsere daga muhallinsu sakamakon bullar kazamin fadan da ake gwabzawa tsakanin sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces a birnin El Fasher fadar mulkin Darfur ta Arewa da ke yammacin kasar, inda jama’a suke takawa da kafa zuwa garin Tawila da ke da nisan sama da kilomita 60, a yanayin da zafin rana ya haura daraja 40 Celsius, wanda ya kai ga wasu daga cikinsu suna mutuwa saboda yunwa da kishirwa, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka bayyana.

Mutanen da suka rasa matsugunansu a “Tawila” da sauran garuruwan yankin Darfur na rayuwa cikin wani yanayi mai ban tausayi, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 991 a yankin na Darfur a tsakanin ranar 15 ga Afrilu zuwa 15 ga Mayu, saboda yunwa da kuma yaduwar wasu cututtuka. A cewar mai magana da yawun hukumar kula da ‘yan gudun hijira a Darfur, Adam Rijal.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments