Rahotanni na cewa mayaƙa fiye da 100 sun riga mu gidan gaskiya sakamakon wani ƙazamin faɗa da aka gwabza tsakanin ƙungiyar ISWAP da Boko Haram a gabar Tafkin Chadi.
Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa jagoran mayaƙan Boko Haram, Buduma na Bakoura wanda aka fi sani da Abu Umaima, sun ƙaddamar da harin ba-zata a kan mayaƙan ƙungiyar ISWAP da ke hedikwatarsu ta Toumbun Gini.
Majiyar ta ce harin na ba-zata ya janyo wa ƙungiyar ISWAP asarar mayaƙa aƙalla 90 yayin faɗan mai tsanani da suka gwabza.
Kazalika, mayaƙan na Boko Haram bangaren sun ƙwace makamai da kayan aiki a yayin yakiyn inda daga bisani suka karɓe iko da yankunan da ke ƙarƙashin ISWAP da suka haɗa da Toumbun Kare da Toumbun Rogo a Ƙaramar Hukumar Abadam.
Wannan karon-batta ta baya-bayan nan dai na cikin jerin munanan hare-hare da aka yi tsakanin ɓangarorin da ke gaba da juna.
Ana iya tuna cewa, a ranar 6 ga Yuli, 2024, mayaƙan Boko Haram sun kai wani ƙazamin hari a sansanin ISWAP da ke Kwatar Shalla Shuwari, inda suka kashe mayaƙan ISWAP 16 tare da kama jiragen ruwa 8, da makamai da dama, da kuma maƙudan kuɗaɗe.
Har ila yau, a wata arangama da aka yi a baya a Dawashi Kwalta tsakanin ɓangarorin biyu, an kashe ’yan ta’addan ISWAP sama da 20, wasu kuma suka nutse a ruwa a ƙoƙarin tsallake kogi.