Memba a majalisar fayyace maslahar tsarin musulunci janar Muhsin Ridha’i ya bayyana cewa; Iran za ta bude sabon Shafin kai hare-hare masu tsanani da rusau idan har abokiyar gaba Amurka ta ci gaba da kawo gare-harenta.”
Janar Ridha’i ya kuma ce; Idan aka shiga wannan Zangon, to ba hari kwantankwacin wanda aka kawo Iran za ta mayar ba, zai zama mafi tsanani.”
Haka nan kuma ya ce; Daga yanzu an kawo karshen lokacin da za a rika hada yaki da kuma tattaunawa a lokaci daya,abinda yake tafe shi ne tsananta hare-hare idan yaki ya ci gaba.
A jiya Juma’a ne dai janar Ridha’i ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi a talabijin ta kasa, inda ya kara da cewa: “A daidai lokacin da ake nunawa jiragen ruwa, hanyoyin da ya kamata su rika bi suna wucewa ta ruwa, sai ga Amurka ta keta yarjejeniyar da aka cimmawa da zummar yin matsin lamba akan Iran.
Janar Ridha’i ya kuma bayyana cewa; An bai wa tawagar Iran da take halartar tattaunawa akan su kare manufofin al’ummar Iran da jajurcewa akan hakan.
Haka nan kuma ya ce, bisa la’akari da halayyar yaudara ta bangaren makiya,to yanzu yanayi ya sauya, domin Amurkawa sun sake tafka wani laifin bisa kuskuren lissafi.
Haka nan kuma ya yi Ishara da yadda abokan gabar suke rusa gadoji da suke hada tsakanin garuruwa da muhimmanci cibiyoyi na amfanin al’umma.
Dangane da manufofin da abokan gabar suke son cimmawa, janar Ridha’i ya kawo abubuwa da dama da dukkaninsu masu yiyuwa ne.
Daga cikinsu da akwai maimaita kuskuren da su ka yi a Isfahan, na aiko da sojoji,ko kuma kai wa ciboyoyin Nukiliya hari da a baya sun kai masu hari.
Bugu da kari janar Ridha’i ya ce da akwai yiyuwar suna son aiko da sojoji ne cikin,su mamaye wani yankin na Iran sannan su shelanta cewa, a zo a tattauna.
Janar Ridha’i ya kuma ce; Zamanin yin tattaunawa a cikin halin yaki ya riga ya wuce.