Ma’ariv: Mutane 104,000 Ne Su Ka Gudu Daga “Isra’ila” Daga 2022-2024

A wani rahoton da jaridar “Ma’ariv” ta buga a jiya Juma’a, ta bayyana cewa; A tsakanin shekarar 2022 zuwa 2024 adadin ‘yan share wuri zauna

A wani rahoton da jaridar “Ma’ariv” ta buga a jiya Juma’a, ta bayyana cewa; A tsakanin shekarar 2022 zuwa 2024 adadin ‘yan share wuri zauna da su ka gudu daga “Isra’ila” sun kai 104,000 saboda dalilai na tsaro da kuma na rabuwar kawuna, sannan kuma da tsadar gidaje.

Jaridar ta ‘yan sahayoniya ta kuma ambaci cewa;Yanayin tsaro da rabuwar kawuna da rashin karfin tattalin arziki na iya sayen gidaje, su ne kadan daga cikin dalilan da suke ingiza mutane 104,000 su ka fice daga Isra’ilan.

Rahoton jaridar ya kara da cewa mafi yawancin wadanda su ka bar “Isra’ilan” sun fito ne daga garin Haifa, Qudus da kuma Tel Aviv.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted