Ministocin Harkokin Wajen Ecowas Sun Fara Taron Share Fage A Birnin Freetown

Ministocin Harkokin Wajen kasashen Afirka ta Yamma mambobi a kungiyar Ecowas sun fara taron share fage a birnin Freetown fadar gwamnatin Saliyo kafin taron shugabannin

Ministocin Harkokin Wajen kasashen Afirka ta Yamma mambobi a kungiyar Ecowas sun fara taron share fage a birnin Freetown fadar gwamnatin Saliyo kafin taron shugabannin yankin da zaa gudanar a karshen wannan mako.

Shugabanin kasashen COWAS za su gudanar da taron Saliyo da nufin zurfafaf tunani wajen magance matsaloli da suka shafi ta’addanci,tsaro da tattalin arziki da siyasa.

Haka zalika ana sa ran shugabanin za su tattauna yiyuwar samar da wata alaka a fanin tsaro tsakanin su da kungiyar kasashen Sahel ta AES.

Ƙungiyar ECOWAS tun bayan ficewar kasashen Nijar ,Mali da Burkina suke iya kokarin ganin an cimma matsaya tsakanin su da wadanan kasashe da nufin magance wasu daga cikin matsaloli da suke fuskanta a kan iyakokin su da cikin gida.

Wani Masani tsaro na ganin cewa samar da alakar tsaron tsakanin bangarorin biyu, abu ne da zai taimaka ta fannoni da dama.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted