Iran : Za Mu Kare Duk Inci Na Kasarmu Har Numfashin Karshe

Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya yi alkawarin cewa Iran za ta kare dukkan yankunanta har sai numfashin karshe a daidai lokacin da Amurka

Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya yi alkawarin cewa Iran za ta kare dukkan yankunanta har sai numfashin karshe a daidai lokacin  da Amurka ke ci gaba da kai hare-hare a kudancin kasar.

Wannan na zuwa ne bayan harin baya bayan nan da Amurka ta kai wanda ya kasha mutum uku a kudancin birnin Bandar Khamir, yana mai cewa jininsu “ba zai taba zuba banza ba.”

A cikin wani sako a shafinsa na X a ranar Juma’a, Araqchi ya nuna juyayi game da kisan fararen hulan uku, yana mai bayyana su a matsayin wadanda basu da wani laifi inda ya kuma jaddada cewa Iran za ta ci gaba da kare kasarta “daga kudu zuwa arewa, kuma daga gabas zuwa yamma” har zuwa numfashinta na karshe.

A don haka a cewarsa ”Za mu kare kowace inci na kasarmu har zuwa numfashinmu na karshe”.

Jawabinsa ya zo ne yayin da hare-haren Amurka a kudancin Iran ke ci gaba da haifar da asarar rayuka da lalata muhimman ababen more rayuwa.

A wani share kuma Ministan Harkokin Wajen Iran Abass Araghchi ya yi ikirarin cewa Isra’ila ta jawo Amurka cikin “yakin da ba a ga ranar karshensa ba, yayin da Amurka ke ci gaba da kai hare-haren sama a kudancin kasar kusan mako guda a jere duk da yarjejeniyar fahimtar juna da aka sanya hannu a watan Yuni tsakanin Tehran da Washington don kawo karshen yakin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted