Iran Ta Rushe Na’uwar Harba Makamai Masu Linzami M142 HIMARS Ta Amurka A Kasar Kuwaiti

A wata sanarwar da IRGC su ka fitar sun bayyana cewa sun rusa na’urar “HiMARS” ta Amurka dake kasar Kuwaiti wacce take amfani da ita

A wata sanarwar da IRGC su ka fitar sun bayyana cewa sun rusa na’urar “HiMARS” ta Amurka dake kasar Kuwaiti wacce take amfani da ita wajen harba makamai masu linzami.

Sanarwar dakarun kare juyin ta kunshi cewa:

  Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

A karkashin mayar da martani, da mayar da hannun kwarya, akan laifukan da Amurka ta tafka a daren jiya, gwarazan mayakan dakarun kare juyi, a karkashin hari karo 15 mai taken “Farmakin Nasara” ta amfani da taken; “Ya Mahdi Ka Riske Ni.” Sun rusa na’urar harba makamai masu linzami ta “ HiMARS” a kasar Kuwaiti. An kai farmakin  da jirage marasa matuki da kuma makamai masu linzami akan cibiyoyin Amurka da dama da kuma na masu adawa da juyi ‘yan koren Amurka da Isra’ila, tare da aikewa da su zuwa jahannama.

Farmakin mayar da hannun kwarya, za ta ci gaba.

“ Nasara, ba daga ko’ina ake samunta ba, sai daga wurin Allah,mai buwaya, ma’abocin hikima.”

A wata sanarwar da dakarun kare juyin musuluncin na Iran su ka fitar sun bayana cewa sun rusa na’urar tsinkayo nesa ta “Radar” mai cin dogon zango mallakin Amurka.

Share

5 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted