Kasashen Rasha Da China Sun Yi Watsi Da Zargin Da Trump Yayi Musu

Rahotanni sun bayyana cewa kasashen Rasha da china sun yi  watsi da zargin da shugaban Amurka Donald Trump yayi na cewa mosko da baijin suna

Rahotanni sun bayyana cewa kasashen Rasha da china sun yi  watsi da zargin da shugaban Amurka Donald Trump yayi na cewa mosko da baijin suna tsoma baki kan harkokin zabe mai zuwa na kasar Amurka

A cikin wani jawabinsa na farko na mintuna 25 da yayi wa alummar Amurka a jiya Alhamis trump ya gabatar da jawabi a fadar white house bayan fitar da wani sabon kuri’a daga Washington post wanda ya nuna cewa farijininsa ya ragu zuwa kashi 37 cikin 100, inda masu kada kuri’a da dama a Amurka suka nuna rashin gamsuwa game da tsadar rayuwa da kuma mummunan yakin da ake yi da iran

A nata bangaren fadar Kremlin ta sanar a yau  jumaa cewa ta yi watsi da zargin da Amurka take yi na cewa rasha na kokarin tsoma baki a harkokin zaben Amurka adaidai lokacin da ake da’awar raunin da ke tare da tsarin zaben.

Ana sa bangaren kakakin maikatar harkokin wajen  kasar china lin jian yayi kira da trump da ya dakatar da wadannan zarge-zargen marasa tushe da yake mata, trump ya zargi makiyan Amurka ciki har da Beijin da tsoma baki a zaben shugaban Amurka na shekara ta 2020

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted