Wanda ya jagoranci sallar juma’a a birnin Tehran Hujjatul-Islam Haj Ali Akbari ya bayyana cewa; Daukar fansar jinin jagora shahidi zai ci gaba har zuwa korar Amurka daga cikin wannan yankin da kuma kawo karshen Haramtacciyar kasar Isra’ila.
Kamfanin dillancin “Mehr” na Iran ya nakalto Hujjatul-Islam Wal Muslimin Muhammad Jawad Haj Akbari yana cewa; Babban dace mu ka yi a rayuwa da mu ka kasance a raye a zamanin bawan Allah na kwarai da shi ne jagora shahidi.
Haka nan kuma limamin juma’ar na Tehran ya kuma ce, jagora shahidi ya kasance wanda matasa su ka amfana daga alabarkatun addu’o’insa, ya kuma yi wa mutane masu tarin yawa tarbiyya akan hanyar kai wa ga Allah.
Limamin juma’ar na Tehran ya bayyana cewa; Jagora shahidi ya shimfida yanayi a cikin kasa na bautar Allah madaukakin sarki cikin tsarkin niyya.
Limamin na juma’ar Tehran ya kuma yi ishara da matsayin ilimi na jagora shahidin, tare da cewa har karshen rayuwarsa bai taba dakatar da neman ilimi ba,kamar kuma yadda ya daukaka matsayar Iran ta fuskar ilimi.