Shugaban kasar DRC ya bayyana cewa kasarsa tana goyon bayan Shirin zaman lafiya da kasashen yankin su ka gabatar da shi, da kuma na duniya domin ganin an kawo karshen yaki a gabashin kasar tasa.
Shugaban kasar ta DRC Filixs Tshekedi ya kuma bayyana cewa yana son ganin dukkanin yarjejeniyoyin da aka kulla na zaman lafiya an yi aiki da su.
Shi dai shugaban kasar ta DRC ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wurin taron zaman lafiya da zummar kawo karshen yake-yake da girmama dokokin kasa da kasa wanda aka yi a birnin Luanda na kasar Angola.
An bude wannan taron ne dai na hadin gwiwa a tsakanin gwamnatin Angola da kuma wata cibiyar majalisar Dinkin Duniya mai kula da ci gaban al’umma,a ranar Alhamis din da ta gabata, ya kuma ci gaba har zuwa jiya Juma’a.
Shugaban kasar ta DRC ya ce; Matsalar tsaro da tabarbarewar rayuwar mutane da ake fama da su agabashin kasarsa, wanda yake da alaka da ayyukan kungiyoyi masu dauke da makamai da hijirar da mutane suke yi, da kuma keta hakkokin bil’adama da tsoma bakin kasashen waje, wani babban kalubale ne ga nahiyar Afirka da kuma kungiyoyin kasa da kasa,ba wai ga kasarsa ita kadai ba.
Shugaba Tshikedi ya ce zaman lafiyar da ake son shimfidawa ya zama wajibi ya kunshi shimfida ikon gwamnati a dukkanin kasar da kare fararen hula da kuma bayar da dama ga ‘yan hijira da su koma gida.