IRGC, Ta Sake Kai Hare Haren Martani A Yankin

Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci na Iran sun samar da kai sabbin hare haren martani a wasu sansanonin Amurka a yankin.

Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci na Iran sun samar da kai sabbin hare haren martani a wasu sansanonin Amurka a yankin.

Sanarwar IRGC ta an hari wata cibiyar sadarwa ta sojojin Amurka a Kuwait da wasu cibiyoyin sadarwa na sojojin Amurka a Bahrain a matsayin ramuwar gayya kan harin da Amurka ta kai wa Iran cikin daren jiya.

A cikin wata sanarwa a wannan Asabar Rundunar Sojin Ruwa ta Iran ta kai hare-hare karo na 19 na Operation Nasr-2, yayin da take ci gaba da rike iko da mashigar Hormuz.

Rundunar IRGC ta kuma yaba wa mutanen Iran saboda ci gaba da goyon baya da juriyarsu.

Kafin hakan dama Rundunar kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta kaddamar da wani gagarumin hari na ramuwar gayya a fadin Yammacin Asiya, inda ta kai hari kan cibiyar sojojin Amurka ta musamman da ke Siriya, wuraren radar na Amurka a Oman, da kuma rumbunan ajiye makamai da na’urorin harba makamai a Kuwait da sanyin safiyar ranar Juma’a.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, Ma’aikatar Hulda da Jama’a ta IRGC ta ce an lalata tsarin radar da wasu jiragen sama masu saukar ungulu na musamman, yayin da aka kashe adadi mai yawa na sojojin Amurka.

Ta kara da cewa harin ya zo ne don daukar fansar jinin sojojin Iran bakwai marasa wadanda suka yi shahada a ranar Laraba a harin sama da Amurka ta kai kan sansanin sojojin Brigade na 388 da ke Bampur, kusa da birnin Iranshahr na kudu maso gabashin kasar.

“Mayakanmu masu jarumtaka suna ci gaba da iko da mashigin Hormuz. Muddin Amurka ta ci gaba da aikata barna, ba za a yarda a fitar da ko digo daya na mai ko iskar gas daga yankin ba,” in ji IRGC.

A wata sanarwa ta daban, IRGC ta ce dakarunta sun kai hari tare da lalata radar sa ido kan jiragen ruwa a Salmah Plateau da kuma radar sa ido ta Amurka da ke Oman.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted