Shugaban Kwamitin Tarayyar ta Afirka (AU) ya bayyana hakan ne a wata ziyarar aiki da ya kai a Burkina Faso.
Mahamoud Ali Youssouf, wanda da farko ya ziyarci Bamako, ya yi kira ga hukumomin rikon kwarya na Burkina Faso da su ci gaba da hadin gwiwa da AU da kuma inganta dangantaka tsakanin Kungiyar Kawancen Sahel (AES) da kuma Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka ta (ECOWAS ko CEDEAO).
Tarayyar Afirka ta yi kira da a bude fagen siyasa, a shirya zabe, da kuma kammala tsarin siyasa da ake gudanarwa.
Shugaban Kwamitin Tarayyar ta Afirka ya je ne da nufin sake jaddada “sake shiga tsakani” na Kungiyar ta (AU) da Burkina Faso, wacce aka dakatar daga tarurrukan siyasa tun bayan juyin mulkin watan Janairun 2022.
Bayan ganawa da Fira Ministan Burkina Faso, Rimtalba Jean Emmanuel Ouedraogo, Tarayyar Afirka ta bayyana fatanta na cewa ci gaba da tsarin siyasa zai haifar da bude fagen siyasa, dawo da jam’iyyun siyasa, da kuma gudanar da zabe.
A bangaren tsaro, Shugaban Hukumar AU ya dage cewa dole ne duk kasashen Afirka su yaki ta’addanci, sannan ya yi kira ga Burkina Faso da Kungiyar kawancen kasashen Sahel (AES) da su inganta dangantakarsu da Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka wacce ta kunshi Burkina Faso, Mali, da Nijar da suka sanar da janyewarsu daga cikin (ECOWAS), a watan Janairun 2024.
AU ta kuma yi kira da a farfado da Tsarin Nouakchott, wanda Tarayyar Afirka ta kaddamar a watan Maris na 2013, wanda ke da nufin karfafa hadin gwiwar tsaro da kuma raba bayanan sirri a yankin Sahel da Sahara.