Majiyar kamfanin dillancin labarun “Reuters” ya bayar da labarun cewa; Sojojin Amurka sun cinye mafi yawancin makamai masu linzami dake cin dogon zango da suke da su a tsawon lokacin yaki da Iran.”
Rahoton na kamfanin dillancin Reuters ya kuma ambato majiyar sojan na Amurka tana cewa; Halin da ake ciki ya jefa tsoro a tsakanin jami’an gwamnatin Amurka na karewar makaman nasu.”
Makaman da ake maganar sun kare, su ne wadanda ake harbawa daga kasa, da ake kira da” MGM-140 ATACMS” sai kuma makaman “Brizm”
Majiyar ta kara da cewa; Amurka ta cinye dukkanin wadannan makaman babu wnada ya saura.”
Ayakin Rasha da Ukiraine, makamin Amurka na ” MGM-140 ATACMS” ya taka rawa wajen kai wa kasar Rasha hare-hare.
Kudin kowane daya daga cikin wadannan makaman masu linzami shi ne Dalar Amurka miliyan daya.
A gefe daya, a wani sako na sirri da kwamandan sojan Amurka a nahiyar turai Alexus Gregory Grynkewich ya aike wa “Pantagon” yana mai cewa; Kayan aiki da suke da su, ba su wadatar ba da za su ci gaba da bai wa “Isra’ila” kariya daga makaman Iran masu linzami.
Jaridar Washington Post ta buga labarin da yake cewa; Idan har ba a sake tura masa wani jirgin yaki ba, to ba shi da zabi, sai ya bai wa Amurka kariya maimakon Isra’ila.”