Jakadan shugaban kasar Rasha na musamman kan al-amuran yaki a Ukraine ya bayyana cewa masu son yaki a cikin shuwagabannin kasashen turai suna zagon kasa ga kokarin shugaba Trump na kasar Amurka yake yi na kawo karshen yaki a Ukraine.
Tashar talabijinn ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Kirill Dmitriev yana fadar haka, a shafinsa na X , inda yake zargin shuwagabannin kasashen turai da hana tsaida yaki a Ukraine.
Dmitriev ya kara da cewa Brussels na zangon kasa ga shirin tsaida yakin tare da dorawa shugaban kasar Ukraine gabatar da bukatun ba zasu taba yiyuwa Rasha ta amince da sub a.
Ya kara da cewa shuwagabannin kasashen Turai suna tsawaita yakin har zuwa lokacinda Al-amura zata sake komawa hannusu bayan sun fita hannun Trump su kuma su fadada yakin.