Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov wanda yake ziyarar aiki a kasar Mozambique ya yi wa gwamnatin kasar tayin taimaka mata ta magance barazar ta’addanci da take fuskanta.
Sojojin kasar ta Mozambique dai suna fada da ‘yan ta’adda a yankin Arewacin kasar na Cabo Delgado dake da arzikin man fetur.
Yankin ya fuskanci hare-hare na ta’addanci daga kungiya mai alaka da alka’ida akan cibiyoyi na fararen hula da na tsaro. Haka nan kuma kungiyar ta rika kashe mutane da ya hada da fille kai,kamar yadda su ka tilasawa dubban mutane yin hijira ta dole.
Lavrov ya ce:
” Muna ci gaba da taimakawa shugaba Chapo akan kokarinsa na tabbatar da zaman lafiya a arewacin kasar, domin ganin an kawo karshen barazanar ta’addanci.
Yankin Cabo Delgado yana da arzikin iskar Gas, da ya sa manyan kamfanonin makamashi na duniya shiga cikin yankin domin fito da shi.
Tun a 2021 ne kasar Rwanda ta aike da sojoji zuwa yankin domin taimakawa kasar Mozambique a harkokin tsaro.
Ministan harkokin wajen kasar Rasha Lavrov ya fara ziyarar aiki ne a nahiyar Afirka,wacce ya faro ta daga kasar Habasha, ya kuma isa kasar Niger.