Rahotonni: Agajin Jin kai Da Ake Jefawa Ta Sama A Gaza Ba Shi Da Tasiri

Jaridar Le Monde ta bayyana cewa: Tallafin kayan da jiragen sama suke saukarwa a Gaza tamkar digon ruwa ne idan aka kwatanta girman bukatun al’ummar

Jaridar Le Monde ta bayyana cewa: Tallafin kayan da jiragen sama suke saukarwa a Gaza tamkar digon ruwa ne idan aka kwatanta girman bukatun al’ummar yankin

Jaridar Le Monde ta ruwaito cewa, ko da yake hukumomin mamayar Isra’ila, a karkashin matsin lamba na kasa da kasa, sun ba da izinin saukar da kayan agajin abinci ta hanyar jiragen sama, amma adadin tallafin takaitacce ne da ba zai magance wata matsala ba.

Le Monde ta kara da cewa: Sakamakon ya bayyana takaitacce ne a daidai lokacin da dubban manyan motoci makare da kayan agaji ke makale a wajen zirin Gaza. Jaridar ta yi bayanin cewa kasashe da dama da suka hada da Jordan, Hadaddiyar Daular Larabawa, Faransa, da Birtaniya, sun fara jigilar kayan agaji zuwa zirin Gaza mako guda da ya gabata ta hanyar amfani da jiragen yaki da ke shawagi a kan yankin Falasdinu.

Faransa za ta yi taimaka da ton 40 a jigila hudu, yayin da Spain za ta sauke tan 12. Sauran ƙasashe, kamar Belgium, Italiya, da Jamus, suma sun sanar da aniyarsu ta shiga ko ba da gudummawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted