Gwamnatin kasar Qatar ta amincewa wata tawaga ta kwararru daga kasar Iran su ziyarsa kasar don ganawa da matuka jiragen yakin kasar guda 3 wadanda aka kamasu su a cikin kwanakin yakin Ramadan na farkon wannan shekarar.
Kamfanin dillancin Tasnim na kasar Iran ya majiyar gwamnatin kasar Iran na cewa, gwamnatin kasar Qatar ta amincewa wata tawagar kwararru su ziyarci matukan jiragen don ganawa da su da kuma ganin lafiyar jikinsu da kuma fara tattaunawa da gwamnati Qatar batun sakinsu.
Labarin ya nakalto Burgediya Janar Muhammad Bakir Zadeh shugaban kwamitin gano fursinonin yaki na sojojin kasar Iran na fadar cewa, bayan ganawa da sojojin tawagar zata bukaci gwamnatin Qatar ta bada dama ga sojojin su yi magana da iyalansu a ginda don su san halin da suke ciki.
Kafin haka dai gwamnatin kasar Iran ta bukaci Qatar ta saki wadannan matuka jiragen yaki, uku , amma gwamnatin Qatar ta musanta sanin wani abu dangane da su, sai dai gwamnatin Iran ta shigar da bukata ga kungiyar Red Cross ta duniya ta cecisu daga hannun Qatar, don nbasu da lafiya , annan ne aka gano inda suke.
Hakama gwamnatin JMI ta bukaci kasar Kuwai ta sharya dama ta ganawa da sojojin Iran da suke tsare a hannunta.
Kafin haka Janar Bakir Zadeh ya bukaci gwamnatin kasar Quwait ta bar Jakadan JMI a kasar ya gana da sojojin kafin wani yazo daga Iran don tabbatar da halin da suke ciki.
Gwamatocin kasashen Qatar da Kuwait sun kama wadannan sojojin Iran ne a cikin yakin da Amurka ta dorawa JMI a farkon wannan shekara.