Jiragen saman Amurka masu zubawa jiragen yaki makamashi a sama samfurin “Boeing KC-135” sun fice daga kasar Bulgaria bayan da Iran ta yi gargadi akan barin Amurkan ta ti amfani da kasarta wajen kawo ma ta hari.
Ministan tsaron kasar Bulgaria Dmitar Stoyanov ya bayyana cewa jiragen biyu na Amurka masu shayar da jiragen yaki makamashi a sama sun bar kasar bayan da su ka yi zaman a garejen lokaci har tsawon wata daya.
Tun da fari majalisar dokokin kasar ta Bulgaria ce ta amince da bukatar Amurka na ajiye jiragen saman guda biyu a cikin kasar da kuma sojojin da yawansu ya kai 250.
Sai dai girke jiragen na Amurka ya sa mazauna yankin yin zanga-zanga da nuna kin amincewa saboda tsoron hare-haren jirage marasa matuki da kuma makamai masu linzami daga Iran.
A wancan lokacin dai Iran ta bakin ma’aikatar harkokin wajenta ta nuna kin amincewa da girke wadancan jiragen a kasar Bulgaria, tare da yin kira ga kasar da ta sake tunani akan batun cikin gaggawa.
Haka nan kuma Tehran ta gargadi ga Bulgaria akan kar ta bari Amurka ta yi amfani da kasarta wajen kawo ma ta hari, domin hakan zai mayar da ita wacce ta yi tarayya wajen kai wa Iran hari.