Mutane Da Dama Sun Bace Sanadiyyar Kifewar Jirgin Ruwa A Kasar Tunisiya

Rahotanni daga kasar Tunisiya sun ambaci cewa mutane 13 sun bace sanadiyyar kifewar wani jirgin ruwa a gabar Ruwan Tunisiya akan hanyar zuwa Italiya.
Jirgin ruwa

Rahotanni daga kasar Tunisiya sun ambaci cewa mutane 13 sun bace sanadiyyar kifewar wani jirgin ruwa a gabar Ruwan Tunisiya akan hanyar zuwa Italiya.

Cibiyar kare hakkin bil’adama ta “al-mirsad” wacce ta bayar da labarin ta kuma ce an yi kokarin ceto da mutane biyu da su ka nutse a cikin Ruwan, daya daga cikinsu yana cikin mummunan yanayi.

Shugaban cibiyar kare hakkin bil’adama, Mustapha Abdulkabir, ya fada wa kamfanin dillancin labarun “Reuters” da safiyar ranar Alhamis ne karamin jirgin ruwa  ya fara tafiya daga kasar ta Tunisiya da zummar zuwa gabar Ruwan Italiya.

Majiyar yankin da lamarin ya faru ta bayyana cewa; Mafi yawancin wadanda suke cikin jirgin Ruwan samari ne da su ka fito daga yankin Binqardan dake kudu masu gabashin Tunisiya.

Sai dai mahukunta a yankin sun ce har yanzu babu cikakken bayani akan adadin wadanda hatsarin ya rutsa da su.

Wannan hatsarin dai ya faru ne, bayan da aka sami koma bayan masu yin hijira daga Tunisiya zuwa kasar Italiya da zumma shiga kasashen turai.

A shekarun bayan kasar Tunisiya ta kasance daya daga cikin muhimman cibiyoyin da masu son shiga cikin kasashen turai suke ratsawa ta cikinta,musamman wadanda su ka fito kasashen Afirka na kudancin Sahara.

Kasashen turai dai suna bayar da kudade ga kasashen Afirka da ruwa ya shiga tsaaninsu da zummar hana masu son yin hijira ketara ruwa domin su shiga cikinsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted