Iran: Zamu Sami Nasara Kan Takunkuman Ta’addanci Na Amurka

Mataimakin ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa kasar Iran zata sami nasara a kan takunkuman ta’addanci wanda Amurka ta dorawa kasar a baya bayan

Mataimakin ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa kasar Iran zata sami nasara a kan takunkuman ta’addanci wanda Amurka ta dorawa kasar a baya bayan nan.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Saeed Khadibzadeh shugaban cibiyar koyon siyasar kasa da kasa na ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana haka ne a jiya a lokacinda yake  halattar taron dangane da ranar tunawa da goyon bayan wadanda ayyukan ta’addanci ta shafa a duniya.

Ya kuma kara da cewa shugaban kasa Dr Pezeshkiyan da sauran bangarorin gwamnati wato Sharia da kuma majalisar dokoki zasu haka kai da mutanen kasar don kawo karshe ko rage tasirin takunkuman tattalin arzikin da Amurka ta dorawa kasar. Kuma daga karshe Iran zata sami nasara a kan Amurka da kawayenta.

Khadibzadeh ya bayyana cewa ba wannan karon farko wanda Amurka ta dorawa kasar takunkuman tattalin arziki ba, amma Iran ta tsallakasu, duk da cewa bazamu ce basu yi tasiri ba, amma sun kasa kaita ga inda take bukata na kifar da gwamnatin kasar.

Daga karshe ya bayyana cewa wadannan takunkuman sabon salon ayyukan ta’addancin ne, wand aba zai gagari gwamnati na mutanen kasar Iran maganceshi ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted