Ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar da cewa sojojin kasar sun yi nasarar kakkabo jiragen sama marasa matuki 328 da Ukirania ta harba a sassa mabanbanta a daren jiya.
Ma’aikatar tsaron kasar ta Rasha ta kuma ce; An kakkabo jiragen ne a tsakanin karfe 8;00 na marece har zuwa karfe 8;00 na safiyar yau Lahadi.
Yankunan da aka kai wa hare-haren sun hada Bilgorod, Tola,Vladmir,Fologo Grad da Cologa.
Yaki a tsakanin kasashen Rasha da Ukirania yana kara tsanani a cikin watannin bayan nan, bayan da hare-haren nasu su ka mayar da hakali akan muhimman cibiyoyi.