Qalibof: Tsaro Mai Cin Gashin Kai A Yankin Ne Kawai Zabi Ga Yankin

Kakakin majalisar dokokin kasar Iran kuma shugaban tawagar tattaunawar kasar Mohammad Bakir Qalibof ya bayyana cewa, ya sami sakonni daga kasashe makobta da dama kan

Kakakin majalisar dokokin kasar Iran kuma shugaban tawagar tattaunawar kasar Mohammad Bakir Qalibof ya bayyana cewa, ya sami sakonni daga kasashe makobta da dama kan cewa suna bukatar sabon tsaron tsaro a yankin bayan da yakin da Amurka da HKI suka dorawa kasar Iran ta lalata tsaro da kuma tattalin arzikinsu a yankin.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Qalibaf yana fadar haka a shafinsa na X a yau Lahadi, ya kuma kara da cewa, sabon tsarin tsaro ne kawai zai samar da zaman lafiya mai dorewa da kuma sake farfado da tattalin arzikin yankin yammacin Asia. Kuma kasashen yankin ne kadai ba tare da shigo da wata kasa daga wajen yankin ba, zasu samar da wannan sabon tsarin. Inji shi.

Ya ce HKI ta sanya dukkan kawayenta a yankin yammacin Asiya cikin matsalolin tsaro da kuma ta tattalin arziki. Tare da farwa kasar Iran da yaki. Ya kuma kara da cewa,  tsarin tsari wanda ya samo asali daga kasashen yankin ne kawai maganin matsalolin da ake ciki.

Kafin haka dai JMI ta sha nanatwa kasashen yankin kan cewa, Amurka ba zata tabbatar da tsaron wata kasa a yankin, ba don kome ba saboda ita ma bata da tsaro a sansanonin sojojinta da ke yankin.

Qalibof yana fadar haka ne a dai dai lokacinda gwamnatin Amurka ta dorawa kasar Iran sabbin takunkuman tattalin arziki, sannan ta yi barazana ga dukkan kasashen duniya su mutunta takunkuman ko kuma su fuskanci fushinta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted