Jagoran ‘Yan Hamayyar Kasar Tanzania Ya Yi Watsi Da Shari’ar Siyasa Da Ake Yi Masa

A ranar Juma’ar da ta gabata ne aka gabatar da jagoran ‘yan adawar siyasar kasar Tanzania Tundu Lissu a gaban kotu domin amsa wasu tambayoyi

jagoran hamayya Tanzania

A ranar Juma’ar da ta gabata ne aka gabatar da jagoran ‘yan adawar siyasar kasar Tanzania Tundu Lissu a gaban kotu domin amsa wasu tambayoyi kamar yadda majiyar kotun ta bayyana.

Lissu wanda yake jagorantar jam’iyyar Chadema an kama shi ne tun a cikin watan Aprilu na 2025 aka zarge shi da laifin  cin amanar kasa, saboda abinda mahukuntan kasar su ka ce, ya ingiza al’umma su kauracewa manyan zabukan da aka yi.

Wannan dai ba shi ne karon farko da aka kama Lissu ba tun bayan komawarsa kasar  daga gudun hijira a 2023, haka nan kuma ya tsallake yunkurin kisan gilla a 2017.

Bayan zaben shugaban kasar da aka yi a shekarar da ta gabata, kasar Tanzania ta fuskanci suka daga kungiyoyin kasa da kasa saboda yadda aka murkushe ‘yan hamayya ta hanayar amfani da karfi. Kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun ce dubban mutane ne aka kashe sanadiyyar zaben na watan Nuwamba.

An girke jami’an tsaro masu yawan gaske a zaman kotun na ranar Juma’ar da ta gabata, yayin da ,magoya bayan jagoran hamayyar su ka Ii cincirindo a wajen kotun.

Haka nan kuma jami’an diplomasiyya da dama sun sami halartar zaman kotun na shekaran jiya Juma’a.

Mai shari’a Dunstan Ndunguru ya bayyana cewa; bayan da kotun ta tsara abinda za a yi shari’ar a kansa, da akwai bukatar Lissu ya bayar da jawabi akan wasu tambayoyi da za a yi masa.

Lissu ya bayyana wa kotun cewa yana da bukatar lauyoyi masu  ba shi kariya su  halarta,amma a lokacin da da yake gidan kurkuku an hana shi saduwa da su.

Jamiyyar adawar ta zargi shugabar kasar Suluhu Hassan da cewa ta mayar da kasar kan turbar tsohon shugaban kasar ta kama-karta da danniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted