Iran: Shugabannin Bangarori Uku Na Gwamnatin Iran Sun Yi Zama A Fadar Shugaban Kasa

Kamfanin dillancin labarum "Irna" ya bayar da labarin cewa, bangarori uku na gwamnatin Iran sun yi taro a fadar shugaban kasa domin tattauna muhimman batutuwa
Taro a fadar shugaban kasar Iran

Kamfanin dillancin labarun “Irna” ya bayar da labarin cewa, bangarori uku na gwamnatin Iran sun yi taro a fadar shugaban kasa domin tattauna muhimman batutuwa da su ka shafi kasa.

Shugaban kasa Mas’ud Pezeshkiyan ya karbi bakuncin shugaban majalisar shawarar musulunci, Muhamma Bakir Kalibaf, da shugaban ma’aikatar sharia HujjatulIslam Gulam Hussai Muhsini Iji.”

Shugaban majalisar shawarar musulunci ta Iran Muhammad Bakir Kalibaf ya bayyana cewa; Taron na yau zai mayar da hankali ne akan batutuwa masu alaka da tattalin arziki da  kuma abubuwan da suke faruwa a cikin wannan yankin.

Haka nan kuma ya kara da cewa mahalarta taron sun amince da daukar matakai da aiki tare domin rage matsin lamba na tattalin arziki akan mutane, da kuma cigaba da taimakawa masu karamin karfi da kare  manufofin kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted