Kakakin dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran Manjo Janar Hossain Muhibbi ya bayyana cewa, sabbin takunkuman tattalin arzikin da Amurka ta dorawa kasar Iran wadanda ta kirasu masu nikews, ya tabbatar da cewa amfani da karfin soje a kan kasar Iran ya gaza, don ai in da Amurka ta sami nasara a kan kasar Iran da kuwa ba bukatar takunkuman tattalin arziki a kanta.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Janar Mohebbi yana fadar haka a wani taro a garin Karaj kusa da nan birnin Tehran, ya kuma kara da cewa a hatta yakin da gwamnatin Amurka da HKI suka dorawa kasar Iran ba yaki ne mai wata manufa ba in banda kashe yara yan makaranta fararen hule da kuma kashe mutanen da basu san hawa ko sauka ba.
Dangane da sabbin takunkuman tattalin arziki a kan Iran kuma, Jnar Muhibbi ya ce, Iran ta saba da takunkuman tattalin arziki fiye da shekaru 47 da suka gabata, kuma a wadan nan sabbin takunkuman tattalin arziki zata tsallakasu kamar yanda ta tsallaka wadanda suka gabace su.
Daga karshe sake dawowa kan takunkuman tattalin arziki masu tsanani ya tabbatar da cewa nuna karfin soje ya gaza kaiwa ga manufofin Amurka da kawayenta, kuma sake dawowan kan takunkuman tattalin arziki ya nuna cewa Amurka bata da wani abu da hannun kuma sai sake nanata makamin da ta yi amfani da shi a kan Iran shekaru fiye da 40 wanda bai yi aiki ba. Kuma ba zai taba yin aiki a kan gwamnati da mutanen kasar ba.