Shuigaban kasar Iran Dr Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa Iran ta bawa duniya mamaki a lokacinda suka nuna karfi da jajircewa kan yakin da Amurka ta dorawa kasar ta tattalin arzki tsaro da kuma mamaya da karfi.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a yau a lokacinda ya je hubbaren Imam Khomainei (a) a kudancin kasar Tehran a yau Lahadi don jadda bai ga marigayi Jagora wanda ya kafa JMI a dai dai lokacinda ake fara makon gwamnati a kasar.
Shugaban ya godewa mataimakinsa da kuma sauran majalisar ministocinsa wadanda suke aiki dare da rana don ganin takunkuman tattalin arziki mafi muni a kan kasar basu yi wani tasirin a zo a gani kan mutanen kasar ba.
Y a ce wadannan takunkuman ba zasu tarwatsa kasar kamar yanda makiya suke nufi ba, kuma ba zasu kai ga manufofinsu n araba kan mutanen kasar ko kuma mutane da gwamnatin kasar ba.
Shugaban ya ce, da farko muna neman uzuri kan wahalhalun da wadannan takunkuman suka sanya a cikin al-amuran rayuwa na mutanen kasar, amma kuma bamu zauna bamu yi kome ba. Ministoci da ma’aiktun gwamnatin daban daban suna aiki dare da rana don rage tasirin takunkuman a kan rayuwar mutanen kasar.