Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi tsokaci kan labaran karya da kafofin watsa labaran Amurka ke yadawa game da tattaunawa da Iran
A matakin da Amurka ta dauka na yada labaran karya game da zaman tattaunawa da Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Kakakin Majalisar Dokokin Iran kuma shugaban tawagar Iran a zaman tattaunawa da Amurka Muhammad Baqir Qalibaf ya tabbatar da cewa: Amurka tana yada labaran karya tare da amfani da kafofin yada labarai don cimma bukatunta na yakin neman zabe, bayan gazawar da ta yi wajen cimma munanan manufofinta ta koma kan dabi’arta ta yada labaran karya marasa tushe a shafukanta na kafafen yada labarai musamman yanar gizo na Axios.
Da yake mayar da martani ga labaran karya da Axios ya buga game da tattaunawar Iran da Amurka, Qalibaf ya dauki lamarin a matsayin wani bangare na yakin kwakwalluwa da Amurkawa suka yi bayan shan kaye mai yawa a aikin soja a mashigar ruwan Hormuz.
Qalibaf ya yi wa yanar gizo na Axios lakabi da babban tushen yada labaran karya da ke fitowa daga Fadar White House na Amurka, a wani rubutu da ya yi a shafinsa na sada zumunta”.