Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Muhammad Bakir Qalibaf ya bayyana cewa, tattaunawa da makiya, wani nau’i ne na gwagwarmaya da makiya, amma dakatar da yakar su da makami kwatakwata faduwa ne a yankin.
Kamfanin dillancin labaran IRNa na kasar Iran ya nakalto Qalibaf yana fadar haka ne a lokacinda yake ganawa da jami’in hulda da jama’a na kjungiyar Hamsa a jiya laraba wato BasimNa’imm. Ya kuma kara da cewa. Mu bama adawa da tattaunawa, muma muna ni, amma tattaunawa a matsayin wata hanya gwagwramaya ce, amma gwagwarmaya ta asali ta makami ne, a duk lokacinda masu gwagwramaya suka ajiye makama sun fadi warwas a gaban makiyansu kenan.
Labarin ya kara da cerwa mun ga abinda ya faru da PLO a shekara 1980 ba lebanon a lokacinda ta ajiye makamanta.