Gholamhussain Darzi jakadan kasar iran a majalisar dinkin duniya ya bukaci kwamitin tsaro na majalisar donkin duniya da yayi tir da harin da kasar Amurka takai kan masu bikin aure a kudancin kasar iran da ya kai ga shahadar mutane 5 ciki har da wani yaro na shekaru 4 da haihuwa da kuma jikkata sama da mutane 70.
Jakadan yayi wannan kiran ne acikin wasikar da ya aikewa sakatare janar din majalisar dinkin duniya Antonio Guterres da kuma shugaban kwamitin tsaron na majalisar dinkin duniya, a jiya labara bayan sabbin hare haren da Amurka ta kai a lardunan dake kudancin kasar wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane 18 tare da jikkata wasu guda 108
Har ila yau ya bayyana cewa an kai harin ne kan masu bikin aure , kuma yayi ishara da cewa amurka ta kai wasu hare hare a gidajen mutane a kauyen kouhestan da sirik a lardin hormozgan.
kasar iran ta yi tir da wannan mummunan hari da kasar Amurka ta kai yace kai hari kan fararen hula da gangan , keta dokokin kasa da kasa ne kuma ana daukarsa a matsayin laifin yaki.