Iraki: Idan Sojojin Amurka Sun Wuce Wa’adi Zamu Kashesu

Daya daga cikin kungiyoyi masu gwagwarmaya a kasar Iraki ta bayyana cewa idan Amurka ta kuskura ta tsallaka ranar da aka sanya zata fidda sojojinta

Daya daga cikin kungiyoyi masu gwagwarmaya a kasar Iraki ta bayyana cewa idan Amurka ta kuskura ta tsallaka ranar da aka sanya zata fidda sojojinta gaba daya daga kasar Iraki, dakarunta zasu kai mata hare hare.

Tashar talabijan ta Presstv a nan kasar Iran ta nakalto Sheikh Akram Al-Kaabi shugaban kungiyar Harkatu Hezbullah Annujaba yana fadar haka a jiya Laraba, ya kuma kara dacewa, muna jira zuwa ranar 30 ga watan satumba ranar da aka sanya a matsayin ranar kawo karshen samuwar  d=sojojin kawance a kasar Iraki. Idan ranar ta wuce sojojin Amurka da suka rage a kasar Iraki sai dais u fice a cikin akwatunan gawaki.

Yace shugaban kasar Amurka Donal Trump ba zai taba samun nasarar wanzar da sojojinsa a kasar Iraki ba, musamman bayan gazawarsu a kasar Iran.

Kafin haka firay ministan kasar Iraki Ali Al-Zaidi ya bayyana cewa a ranar 30 ga watan satumba da muke ciki ne sojojin kawance wadanda suka hada da sojojin kasar AMurka zasu kawo karshen samuwarsu a kasar Iraki. Don haka a ranar 30 ga watan satumba zamu shelanta ikon kasar Iraki a kan dukkan yankunan kasar.

Al-Zaidi ya bayyana haka ne a ranar 24 ga watan Augusta , a wanitaro na maulidin manzon All..(s) a birnin Bagdaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted